Shugaba Karzai ya fara ziyarar kwana hudu a Amurka

Shugaba Karzai da Obama
Image caption Shugaba Hamid Karzai da Barrack Obama

Shugaban kasar Afghanistan Hamid Karzai, ya isa birnin Washington, domin gudanar da wata tattaunawa, da nufin farfado da dangantakar dake tsakanin kasar da Amurka, wadda ta fuskanci kalubale a baya bayan nan.

Mr Karzai zai gana tare da shugaba Obama a gobe,ranar laraba.

Jakadan Amurka a Afghanistan Karl Eikenberry, ya musanta cewa akwai sabani tsakanin kasashen biyu.

Sai dai wakiliyar BBC ta ce a watan maris din daya gabata gwamnatin shugaba obama ta rika amfani da lafazi mai karfi kan shugaban karzai abun da ya kaiga sukar shugaban a bainar jama'ar.