Baraka ta sake kunno kai a yunkurin kafa jamiyyar Mega party

Taswirar Najeriya
Image caption Taswirar Najeriya

Jam'iyyar Labour Party a Najeriya ta bayyana cewa, a yanzu ta janye daga yunkurin nan na kafa wata babbar jam'iyyar kawancen 'yan adawa, ta Mega Party.

Yunkurin kafa babbar jam'iyyar na daga cikin matakan da kawancen wasu jam'iyyun adawa a Najeriyar suka kudiri anniyar dauka, domin kalubalantar jam'iyyar PDP mai mulki.

A kwanakin baya ne, tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Alhaji Atiku Abubakar, ya fice daga jam'iyyar AC, wadda ita ma ke cikin wannan yunkuri na kafa babbar jam'iyyar ta Mega Party, ya sake komawa jam'iyyar PDP mai mulki.

Don haka wasu ke ganin yadda jam'iyyu, ko kuma wasu kusoshi a cikin wannan yunkurin ke janye jikinsu, a matsayin wani karin koma-baya, a kokarin kafa wata babbar jam'iyyar da zata ja da PDPn mai mulki, wadda shugabanninta ke cewa zata shafe shekaru aru aru tana mulki a kasar.