Najeriya ce ta biyu wajen mutuwar mata masu juna biyu

Wasu mata a Najeriya
Image caption Wannan matsalar ta dade tana cima jama'a tuwo a kwarya a Najeriya

Sakamakon wani bincike da jami'ar California dake Amurka, da kuma ta Ahmadu Bello Zaria a Nijeriya suka gudanar, ya nuna cewar, Najeriya ita ce ta biyu bayan kasar India, cikin kasashen da ke fama da matsalar mutuwar mata masu juna biyu.

Kuma arewa maso gabashin kasar shi ne inda lamarin ya fi kamari, inda kimanin mata dubu daya da dari biyar ke rasa rayukansu daga cikin kowadanne dubu dari, a bisa wannan dalili.

Hakan ya sa wasu manyan kungiyoyi na duniya, suka dukufa wajen daukar matakan ganin an rage wannan matsala.

Misali na baya bayannan shi ne wani taro da wata kungiyar bincike da samar da ci gaba wato DRP ta shirya na wuni daya a Kano, inda ta gayyato malaman addinin musulunci da sarakunan gargajiya na arewacin Kasar dan tattaunawa kan irin gudunmuwar da za su bayar wajen kawar da matsalar.

Mahallat taron dai sun yi amannar cewa malaman addini da sarakuna da hukumomi nada rawar takawa wajen shawo kan wannan matsalar.