An sabunta: 18 ga Mayu, 2010 - An wallafa a 13:50 GMT

Zan tsaya takara a 2011- Buhari

Garmaho

Tsohon shugaban Najeriya, Janar Muhammadu Buhari mai ritaya, ya tabbatarwa BBC cewa, idan jam'iyyar sa ta CPC ta bashi tikiti, to zai tsaya takarar shugaban kasa a zaben shekara ta 2011.

Janar Buhari ya bayyana haka yayin da ya kai ziyara a dakin watsa labaranmu na London. A wannan makon ya gabatar da takarda a jami'ar Oxford akan kalubalen da siyasar Najeriya ta fuskanta a cikin shekaru goman da suka gabata.

Sau biyu Janar Muhammadu Buharin na tsayawa takarar shugabancin Najeriya ba tare da yayi nasara ba. Ya shigar da kararaki a kotu akan zargin cewa an tafka magudi a lokacin zabubukan.

BBC navigation

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.