An sabunta: 18 ga Mayu, 2010 - An wallafa a 19:53 GMT

Harin Bom a Afghanistan

Harin Bom a Afghanistan

 • 'Yan sandan Afghanistan na duba a harin bom ya yi wa barna
  Wani harin kunar bakin wake da aka kai Kabul babban birnin Afghanistan, yayi sanadiyar mutuwar mutane akalla sha takwas ciki har da sojojin Amurka biyar.
 • Kungiyar Taliban ta dauki alhakin kai harin bom din
  Kungiyar Taliban ta dauki alhakin kai harin bom din, inda aka hari wasu jerin gwanon motocin sojin kungiyar tsaro ta NATO.
 • Wadanda suka jikkata na samun kulawa a asibiti
  Akalla mutane 50 ne suka jikkata a harin ciki har da mata da kananan yara. Wasunsu dai fasinjoji ne a cikin motar bas din da ke kusa da wajen.
 • Soji na duba mora bas din da harin ya rutsa da shi
  Wani mutum da ya gane wa idonsa lokacin da aka kai harin, ya ce bom din ya daddasa rudani a wajen bayan ya tashi.
 • Ana sanya gawawwaki a mota
  Bayan an killace yankin, an kai wadanda suka jikkata asibiti, sannan aka sanya gawawwaki a motar soji.
 • Sojoji rike da bindiga
  Shugaban Afghanistan Hamid Karzai ya yi Allah wadai da harin, inda ya bayyan shi da cewa abin kaico da bacin rai ne.

BBC navigation

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.