An sabunta: 28 ga Mayu, 2010 - An wallafa a 10:49 GMT

Hadarin jrigin kasa a Indiya

Hadarin jirgin kasa a Indiya

 • Hadarin jirgin kasa a Indiya
  Akalla mutane sittin da biyar ne suka rasa rayukansu, wadansu da dama kuma suka samu raunuka bayan wasu jiragen kasa biyu sun yi taho-mu-gama a kasar Indiya.
 • Hadarin jirgin kasa a Indiya
  Hakan ya faru ne bayan wani jirgin kasa na fasinja wanda ya tashi daga Mumbai zai je Calcutta ya saki layin dogon da ya ke kai ya hau kan hanyar wani jirgin mai dauke da kaya.
 • Hadarin jirgin kasa a Indiya
  Hadarin dai ya auku ne da duku-duku lokacin da jirgin kasan na Gyaneswari Express ke tafiya a wani yanki da babu kowa a jihar Bengal ta Yamma.
 • Hadarin jirgin kasa a Indiya
  Jami'ai sun ce matukin jirgin bai kula cewa an lalata layin dogon ba saboda gari bai gama wayewa ba.
 • Hadarin jirgin kasa a Indiya
  Taragai goma sha uku ne dai na jirgin fasinjan suka zame daga kan dogon da suke suka hau hanyar da jirgin kayan, wanda ya taso daga Calcutta zuwa Mumbai, ke tafiya.
 • Hadarin jirgin kasa a Indiya
  Masu aikin ceto na ta kokarin ganin sun ceto mutanen yayin da aka aika jirage masu saukar ungulu domin su debi wadanda suka yi rauni zuwa asibiti.

BBC navigation

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.