Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayi Riga: Me ke kawo yawan mutuwar mata wajen haihuwa?

Image caption Dakin haihuwa a wani kauye

Wata kiddidiga ta majalisar dinkin duniya ta nuna cewa a duk shekara mata dubu dari 5 ne ke mutuwa a duniya, sakamakon matsalolin da suke cin karo da su a lokacin haihuwa ko kuma a lokacin da suke da juna biyu.

Jumhuriyar Nijar dai na kan gaba a duniya wajen yawan mace-macen mata a lokacin haihuwa, inda kiddidiga ta nuna cewa mata dubu daya da dari takwas ke mutuwa daga cikin mata dubu dari daya dake haihuwa.

A Najeria kuwa an kiyasta cewa mata dubu hamsin da hudu ke mutuwa a shekara, a sakamakon matsalolin da suke cin karo da su a lokacin haihuwa ko kuma a lokacin da suke da juna biyu.

To don jin karin bayani kan dalilai da ke janyo wannan matsala ta mace-macen mata a lokacin haihuwa da kuma yadda za a rage kaifin ta, mun gayyato kwararru - wato likitoci daga bangaren Gwamnati da kuma wata kungiya mai zaman kanta dake taimakawa wajen yaki da wannan matsala a Najeriya.

Jami'an daga bangaren Najeriya sun hada da Hajiya Hannatu Bello, jami'a a ma'aikatar lafiya ta Najeria, da kuma Dr Faruk Jega, na kungiyar agaji ta Pathfinder a Najeria Sannan a Jumhuriyar Nijar, muna tare kai tsaye da Dr Yaro Asma Gali, Direktar sashen kula da lafiyar mata da kananan yara a ma'aikatar lafiya ta Nijer din. Haka kuma muna da dinbin masu saurare da suka shiga cikin shirin.