An sabunta: 28 ga Mayu, 2010 - An wallafa a 10:00 GMT

'Yan gudun hijira a Somalia

Sansanin 'yan gudun hijira a Somalia

 • Sansanin 'yan gudun hijira a Somalia
  Rashin kyakyawan tsaro a Somalia ya sanya mutane da dama da yawan za su kai sam da miliyan guda sun bar gidajensu sun koma zama wani sansani da ke yankin Garowe a Puntland.
 • Sansanin 'yan gudun hijira a Somalia
  Samira Tima Buule da iyalanta sunyi sama na tsawon shekaru hudu a sansanin. Babu ban daki a sansanin kuma suna fuskantar karancin abinci.
 • Sansanin 'yan gudun hijira a Somalia
  Mutane a sansanin suna rayuwa sansanonin goma sha daya a yakin Garowe. Kuma yawancin su na aikin kwashe shara ne da kuma wanke kaya.
 • Sansanin 'yan gudun hijira a Somalia
  Ahmed Jamma a baya na da dabbobi da za su kai dari hudu, amma a yanzu haka sun koma hamsin.
 • Sansanin 'yan gudun hijira a Somalia
  Mista Jamma ya ce bai san yadda zai kula da iyalinsa ba saboda ba shi da wani aiki, kuma dabbobinsa sun kare.
 • Sansanin 'yan gudun hijira a Somalia
  Hukumar bada agaji ta tarrayarTurai ta kashe milyoyin euro domin yin rigakafi ga dabbobi a sansanin domin taimakawa 'yan gudun hijira.
 • Sansanin 'yan gudun hijira a Somalia
  Mikayaya a sansanin na bukatar akalla dabbobi tamanin ne kowanen su, domin kulawa da kansu. Hukumar basa agaji ce ta tarrayar Turai ta samarda hotunan.

BBC navigation

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.