An sabunta: 18 ga Yuni, 2010 - An wallafa a 14:21 GMT

Hotunan mata masunta na garin Lekki

 • Mata Masunta
  Lekki Jetty, karamin garin masunta ne dake gabar tekun jihar Legas, a kudu maso yammacin Najeriya.
 • Mata Masunta
  Mata su ne manyan dillalan kifi a garin, maza kuma aikin kamo kifin. Mazan kan yi wanka a wannan dandamalin bayan kama kifi.
 • Ade Cap wani masunci
  Ade Cap ya ce a kullum yana kamun kifi. Shi dai daya daga cikin masunta ne dake garin na Lekki da ya riga ya kama kifi da safe.
 • Mata Masunta
  Da zarar matan sun samo kwando-kwandon kifin, sukan rarraba shi bisa girman kowanne kifi da kuma nau'insa.
 • Mata masunta
  Nan wasu mata biyu ne suke kankare kifi a kwando da wani kwastoma ta saya. Za a iya ganinta zaune a shagon da ke bayansu.
 • Mata masunta
  Nan kuma wasu mata biyu ne ke wasa da wasu damo biyu da aka kamo da safe a daji, domin nishadantar da kansu.
 • Mata masunta
  Damo a Afrika dai kan kai tsawon taku tara kwatankwacin mita biyu da dugo bakwai, suna da karfi da kuma kaifin hakora.
 • 'Ya'yan masunta
  Wasu daga cikin 'ya'yan mata masuntan sun dawo daga makaranta, abin da yake kara yawan hayaniyar da akan yi fama da ita a yankin.
 • Wata matar masunci
  Nan wata matar masunci ce, ke tafiya domin taro mijinta da ya dawo daga kamun kifi. Lola Akimde ce ta dauko hotunan.

BBC navigation

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.