Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayi Riga: Kaidojin zabe a jamhuriyar Nijar sun dace?

A jamhuriyar Nijar, dokokin da gwamnatin mulkin soja ta amince da su, wadanda suka hana amfani da takardar haihuwa wajen sabunta rajistar zabe, na haifar da kace-nace.

A karkashin sabbin ka'idojin, ya kamata duk mai son a yi masa rajista, to ya kasance yana da ko dai katin shaidar zama dan kasa, ko fasfo, ko lasisin tukin mota, ko katin fansho, ko katin shaidar zama a kasashen waje.

Sai dai wasu na ganin cewa wannan mataki tamkar wani kokari ne na hana masu yancinsu na kada kuri'a.

Kwamitin rubuta manyan dokoki wanda gwamnatin ta kafa, shi ne ya rubuta sabon kundin zaben. Daga baya kuma, kwamitin tuntubar juna na Conseil Consultatif National, ya yi muhawara a kansa, tare da amincewa da shi - kafin daga bisani shugaban mulkin sojan Niger din, Janar Salou Djibo, ya rattaba hannu a kan kundin zaben.

Mutane kimanin dubu dari takwas ne ake son yiwa rajistar, domin shigar da su a cikin tsohuwar rajistar da ke kunshe da sunayen mutane miliyan shidda.

Tuni aka fara aikin rajistar, wanda ake sa ran kammalawa a karshen wannan makon, amma akwai rahotannin dake cewa rashin takardun da ake bukata, ya hana dimbin jama'a yin rajistar.

To a filinnmu na Ra'ayi Riga na wannan makon, mun gayyato wasu baki da suka hada da Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta Niger (ko kuma CENI), watau mai shari'a Abdurrahmane Gousmane; da Malam Bazoum Mohammed, mataimakin shugaban jam'iyyar PNDS-Tarayya, kuma mamba a kwamitin tuntubar juna na kasa.

Akwai kuma Malam Sabo Saidu, na jam'iyyar MDC-Yarda - daya daga cikin tsoffin jam'iyyu masu mulki, na kawancen AFDR, wadanda sojoji suka yi wa juyin mulki. Sannan akwai dimbin masu saurare da suka shiga shirin.