An sabunta: 5 ga Agusta, 2010 - An wallafa a 14:21 GMT

Yaran da ambaliyar ruwa ta rusta da su a Pakistan

Yaran da ambaliyar ruwa ta rutsa da su a Pakistan

 • Yaran da ambaliyar ruwa ta rutsa da su a Pakistan
  Majalisar dinkin duniya ta yi kiyasin cewa ambaliyar ruwan da ta faru a Pakistan ta shafi kimanin mutane sama da miliyan hudu. Ahmed Reza ne ya dauko mana hotuna.
 • Yaran da ambaliyar ruwa ya rutsa da su a Pakistan
  Ambaliyar ruwan ta mamaye yankuna da dama a kudancin Punjab. A arewa maso yammacin kasar dubunnan jama'a suna matukar bukatar ruwa da abinci.
 • Yaran da ambaliyar ruwa ya rutsa da su a Pakistan
  Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon, ya tura da jakada na musamman Pakistan din domin taimakawa wajen neman agaji daga kasashen duniya.
 • Yaran da ambaliyar ruwa ya rutsa da su a Pakistan
  Sassa daban-daban na tsakiya da kuma kudancin Pakistan na fama da wannan masifa ta ambaliyar ruwa wacce ta yi sanadiyyar mutuwar dubban mutane.
 • Yaran da ambaliyar ruwa ya rutsa da su a Pakistan
  Ambaliyar ta tilastawa miliyoyin mutane barin gidaje, kuma babban abin da ya fi damunsu shi ne rahin abinci.
 • Yaran da ambaliyar ruwa ya rutsa da su a Pakistan
  Wadansu masu kai ajagajin gaggawa na kai agajin , sai dai dubban jama'a sun ce basu samu wani agajin a zo a gani ba.
 • Yaran da ambaliyar ruwa ya rutsa da su a Pakistan
  Shugaban masu bada agajin gaggawa na majalisar Dinkin Duniya, Manuel Bessler, ya ce halin da mutanen da basu samu abincin ba suka samu kansu a ciki abin dubawa ne.
 • Yaran da ambaliyar ruwa ya rutsa da su a Pakistan
  Manuel Bessler ya ce suna duba wannan batun ne musamman ta yadda ya shafi wadanda suka rasa gidajensu, da kuma sauran abubuwan bukatunsu.
 • Yaran da ambaliyar ruwa ya rutsa da su a Pakistan
  Zai dauke su wasu makonnin kafin samun inda za a tsugunar da su, inda za a samar musu da tantuna, da kuma wajen kwana.
 • Yaran da ambaliyar ruwa ya rutsa da su a Pakistan
  Shugaban majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki Moon, ya aika da manzo na musamman, Jean-Maurice Ripert, don neman goyon bayan kasashen duniya wajen agazawa kasar ta Pakistan.

BBC navigation

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.