Hotuna: Zabtarewar kasa a China

Hasashen yanayi na nuna cewa ruwan sama ba kakkautawa zai ci gaba da sauka a arewacin kasar China, yayinda ake ci gaba da kokarin gano mutanen da zabtarewar laka ta shafa.

Zabtarewar kasa a China
Bayanan hoto,

Hasashen yanayi na nuna cewa ruwan sama ba kakkautawa zai ci gaba da sauka a arewacin kasar China, yayinda ake ci gaba da kokarin gano mutanen da zabtarewar laka ta shafa.

Bayanan hoto,

Zabtarewar kasar yayi sanadiyyar rasuwar mutane fiye da dari bakwai a yankin Gansu. Mutane fiye da dubu da 100 ne suka bace.

Bayanan hoto,

Cibiyar kula da yanayi na China ta ce yankin na daya daga cikin wuraren da mahaukaciyar guguwar typhoon Dianmu za ta kai gare su.

Bayanan hoto,

Wakilin BBC ya ce wata mata Jang Shing Shek ta zauna a kan wata laka tana ta kuka, ta yi kwanaki ukku a wurin, yar uwanta na daya daga cikin mutane talatin ko sittin da lakar ta binne.

Bayanan hoto,

Lakar hadi da manyan duwatsu, sun ratsa garin Zhouqu dake lardin Gansu ranar Lahadi inda suka rufe mutane da dama dake cikin gidajensu.

Bayanan hoto,

Ma'aikatan ceto da sojoji suna ta tona baraguzan gine-gine yayinda suke kokarin janye ruwan da suka kwanta a wurin, wanda ke barazana ga rayukan jama'a

Bayanan hoto,

Masu hasashen yanayi sun yi gargadin cewa yanzu yankin na fuskantar barazanar saukar ruwan sama hadi da guguwa.