An sabunta: 13 ga Agusta, 2010 - An wallafa a 11:00 GMT

Al'ummar Darul Islam a kauyen 'Ka, Tsallake'

Kauyen 'Ka, Tsallake'

 • Kauyen 'Ka tsallake'
  A watan Agustan bara ne dai hukumomi a Najeriya suka tilastawa jama'ar da ke zaune a garin Darul Islam a karamar hukumar Mokwa ta jahar Niger barin wajen da suka shafe shekaru da dama suna zaune da iyalensu. Yusuf Ibrahim Yakasai ne ya dauko mana hotunan.
 • Kauyen 'Ka tsallake'
  Tashin mutanen da aka yi dai ya tilsata musu komawa garuruwansu na asali bayan da dama daga cikinsu sun debe kaunar sake komawa domin zama.
 • Kauyen 'Ka tsallake'
  Amma duk da haka mutanen kauyen Ta tsallake dake karamar hukumar Takai sun ce sun fuskanci kalubalen samun wajen zama kafin daga baya su yanke shawarar tunkarar gonaki a tsakiyar damuna domin samun wajen da zasu zauna.
 • Kauyen 'Ka tsallake'
  Shugaban karamar hukumar ta Takai Alhaji Muhammad Baffa ya musanta cewa anyi wani alkawari na samarwa mutanen wuraren zama, kasancewar babu wani umarni da aka basu a rubuce daga sama na cewa su samarwa jama'ar wajen zama.
 • Kauyen 'Ka tsallake'
  Shugaban ya kara da cewa a yanzu ma suna kaffa kaffa da mutanen, saboda rahoton da suka samu na cewa mutanen suna kara yawa, inda suke samun baki daga sassan daban daban.
 • Kauyen 'Ka tsallake'
  Sai dai hukumomin tsaro sun ce basu da wata masaniya dangane da hakan.
 • Kauyen 'Ka tsallake'
  Shekara guda bayan da aka rabasu da garin Darul Islam babban abinda tsofaffin mazauna garin suke bege shi ne, zaman da suka yi a garin.
 • Kauyen 'Ka tsallake'
  Mazauna garin sunce a yanzu babu abinda ya ke ci musu tuwo a kwarya kamar yadda aka yi musu korar kare daga wajen da suka sakankance dashi, ba tare da a cewarsu sun tsarewa kowa komai ba.
 • Kauyen 'Ka tsallake'
  Mazauna garin dai sun ci gaba da sana'arsu ta noma da kuma kiwon dabbobi.

BBC navigation

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.