An sabunta: 25 ga Agusta, 2010 - An wallafa a 10:38 GMT

Malalar ruwa a makarantar Firamare a Kano

Malalar ruwa a makarantar firamare a Kano

 • Malalar ruwa a makarantar firamare a Kano
  A jihar Kanon Nigeria, kimanin ajujuwa 14 ne yanzu haka aka hakura da yin karatu a cikinsu a wata makarantar Framare dake unguwar Hotoro, cikin karamar hukumar Nasarawa mai suna Hotoron Arewa. Yusuf Ibrahim Yakasai ne ya dauko mana hotunan.
 • Malalar ruwa a makarantar firamare a Kano
  Hakan kuwa ta farune saboda ruwa dake malala cikin ajujuwan tare da mamaye harabar makarantar, abinda hakan a cewar wasu iyaye da dalibai, yakan tilasta yin fashin karatu na kwanaki akalla uku.
 • Malalar ruwa a makarantar firamare a Kano
  Makarantar dai itace babbar Framare a yankin, kuma a cewar wasu iyaye makarantar na da dalibai kimanin dubu uku.
 • Malalar ruwa a makarantar firamare a Kano
  Ana dai danganta wannan matsala da rashin magudanan ruwa a kewayen makarantar, sannan kuma gininta ya yi kasa.
 • Malalar ruwa a makarantar firamare a Kano
  To amma hukumomin jahar sun ce nan ba da jimawa ba wannan matsalar zata zama tarihi, domin kuwa sunce a kwana kwannan za'a fara aikin gyaranta.

BBC navigation

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.