An sabunta: 8 ga Satumba, 2010 - An wallafa a 09:48 GMT

Takaddama akan sabuwar kasuwar Minna

Takaddama akan sabuwar kasuwar Minna

 • Takaddama akan sabuwar kasuwar Minna
  A garin Minna da ke jihar Nejan Nigeria kuma wasu `yan kasuwa ne ke kokawa dangane da matakin da hukumomi suka dauka na dage babbar kasuwa garin zuwa wani sabon wuri a cikin karamar hukumar Cancaga. Wani mai saurarenmu ne ya turo mana hotunan.
 • Takaddama akan sabuwar kasuwar Minna
  Kimanin `yan kasuwa dubu ne ke kukan cewa ba su samu shaguna ba a sabon matsugunin, kuma hakan ta tilasta musu jibge kayayyakinsu a gidajensu.
 • Takaddama akan sabuwar kasuwar Minna
  'Yan kasuwar dai sun ce suna cikin wani hali na tsaka-mai-wuya saboda abin ciyar da iyalansu ma na nema ya gagare su.
 • Takaddama akan sabuwar kasuwar Minna
  Wasu `yan kasuwar, da aka daga su daga babbar kasuwar da ke tsakiyar garin Minna, zuwa sabon wurin, na ganin cewa ba ba alheri ba ne a gare su, saboda kawo yanzu ba su samu shaguna ba a sabon wurin.
 • Takaddama akan sabuwar kasuwar Minna
  Karamar Hukumar Chanchaga tace an yi tanadin isassun shagunan da za su wadatar da `yan kasuwar, sai dai ta yi zargin cewa wasu daga cikin ma`aikata ne suka yi ha`inci a cikin al`amarin.
 • Takaddama akan sabuwar kasuwar Minna
  Sai dai wasu na zargin cewa an sayi sabon wurin da aka tsugunar da `yan kasuwar ne daga wani dan uwan gwamnan jihar na jini da nufin buda masa hanyar samun abin duniya, amma karamar hukumar ta musanta.

BBC navigation

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.