An sabunta: 23 ga Satumba, 2010 - An wallafa a 13:16 GMT

Taron nemo mafita ga wasu kasashen Afrika

Taron nemo mafita ga wasu kasashen Afrika

 • Taron nemo mafita ga Najeriya
  A Najeriya, a ranar Alhamis ne wasu kasashe16 da suka samu `yancin kai tare da Najeriyar suka fara wani taro da nufin duba irin kalubalen da suka fuskanta a baya da wadanda suke fuskanta yanzu da kuma hanyoyin shawo kansu.Ibrahim Isa ne ya dauko hotuna
 • Taron nemo mafita ga Najeriya
  Taron dai kamar yadda mahukuntan Najeriya suka bayyana an shirya shi ne domin ya samar da wani zaure da kasashe takwarorin Najeriya wajen samun `yancin kai a shekarar 1960 za su zauna su yi waiwaye tare da tattaunawa a kan kalubalen da suka fuskanta a baya da wadanda suke cin karo da su.
 • Taron nemo mafita ga Najeriya
  Dr Shamsuddeen Usman shi ne Ministan tsare-tsaren Najeriya, kuma yace babban kalubalen da kasashen ke fuskanta a baya shi ne na siyasa, amma yanzu kusan kowa ya koma tafarkin dimokradiyya. Abinda yake damunmu shi ne talauci da habaka tattalin arziki.
 • Taron nemo mafita ga Najeriya
  Tun a farkon taron, wanda ake sa ran zai kwashe kwanaki uku, mahalarta, kama daga jami`an gwamnatocin kasashen zuwa kwararru, duka sun yi ittifakin cewa kasashen sun kwashe shekaru hamsin da samun `yancin kai amma al`umominsu na fama da talauci. Don haka akwai bukatar a samo hanyoyin habaka su cikin gaggawa.
 • Taron nemo mafita ga Najeriya
  Sai dai wasu masanan sun bayyana ra`ayin cewa cutar da ke addabar kasashen ba boyayyi ba ce, sai dai tana da wuyar magani matukar matakan da kasashen ke dauka ba su wuce irin wadannan bukukuwa ba.Kamar yadda Farfesa Munzali Jibril ya bayyana.
 • Taron nemo mafita ga Najeriya
  Masanan dai sun bayyana cewa akwai bukatar shugabannin kasashen su tara hankalinsu a wuri guda, su tambayi kansu ko wane gado za su bar wa `ya`yansu da jikokinsu nan da shekaru hamsin masu zuwa ba shagulgula ba.

BBC navigation

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.