An sabunta: 26 ga Satumba, 2010 - An wallafa a 20:57 GMT

Hotunan tsofaffin shugabanin Najeriya

Hotunan tsofaffin shugabanin Najeriya

 • Hotunan tsofaffin shugabanin Najeriya
  Tsaffin shugabannin Najeriya, daga hagu zuwa dama akwai Firimiyan Yamma Cif Obafemi Awolowo; Alan Lennox Boyd sakataren Turawa; Alhaji Ahmadu Bello Sardaunan Sokoto, Firimiyan Arewa Sir James Robertson, Gwamna janar na Najeriya a lokacin mulkin Turawa da kuma Dr Nnamdi Azikiwe Shuagaban kasa na farko.
 • Hotunan tsofaffin shugabanin Najeriya
  Sir Abubakar Tafawa Balewa ya zamo Firi Ministan farko na Najeriya bayan da kasar ta samu 'yancin kai daga Turawan mulkin mallaka na kasar Ingila
 • Hotunan tsofaffin shugabanin Najeriya
  Janar Yakubu Gowon ya shugabanci Najeriya ta hanyar soji daga shekara ta 1966 zuwa 1975.
 • Hotunan tsofaffin shugabanin Najeriya
  Janar Murtala Ramat Muhammad ya shugabanci Najeriya daga shekarar 1975 zuwa shekarar 1976.
 • Hotunan tsofaffin shugabanin Najeriya
  Olesegun Obasanjo ya shugabanci Najeriya a shekarun 1976 zuwa 1979 a matsayin soja, sannan aka zabe shi ya sake zamowa shugaban faras hula daga shekarun 1999 zuwa 2007.
 • Hotunan tsofaffin shugabanin Najeriya
  Alhaji Shehu Shagari ya shugabanci Najeriya a jamhuriya ta biyu daga shekarun 1979 zuwa shekara ta 1984.
 • Hotunan tsofaffin shugabanin Najeriya
  Janar Muhammadu Buhari ya shugabanci Najeriya ta hanyar soji daga shekarar 1984 zuwa shekara ta 1985.
 • Hotunan tsofaffin shugabanin Najeriya
  Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya shugabanci Najeriya daga shekarar 1985 zuwa shekarar 1993.
 • Hotunan tsofaffin shugabanin Najeriya
  Janar Sani Abacha ya shugabanci Najeriya daga shekarun 1993 zuwa shekarar 1998.
 • Hotunan tsofaffin shugabanin Najeriya
  Janar Abdussalami Abubakar ya shugabanci Najeriya daga shekarar 1998 zuwa 1999, inda ya mayar da kasar kan tafarkin dimokradiyya.
 • Hotunan tsofaffin shugabanin Najeriya
  Alhaji Umaru Musa Yar'adua ya shugabanci Najeriya daga shekarar 2007 zuwa shekara ta 2010, inda Allah ya yi masa rasuwa bayan yayi fama da doguwar jinya.
 • Hotunan tsofaffin shugabanin Najeriya
  Shugaba Goodluck Jonathan ya zamo shugaban Najeriya a shekara ta 2010, bayan rasuwar marigayi shugaba Umaru Yar'adua.

BBC navigation

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.