An sabunta: 11 ga Oktoba, 2010 - An wallafa a 10:32 GMT

Nijar ta yiwa Masar bazata

Nijar ta yiwa Masar bazata

 • Nijar ta yiwa Masar bazata
  Zakaran kwallon Afrika Masar ta sha kashi a wajen Nijar daci daya me ban haushi a wasan da aka buga ranar Lahadi a birnin Niamey. Idy Baraou ne ya dauko mana hotuna
 • Nijar ta yiwa Masar bazata
  Tawagar Menas din ta samu galaba dinne a wasan rukunin G na gasar cin kofin kasashen Afrika da za a buga a shekara ta 2012.
 • Nijar ta yiwa Masar bazata
  Ouwa Moussa Maazou wanda ke taka leda a Faransa shi ne ya zira kwallon bayan an samu kuskure a tsakanin 'yan bayan Masar.
 • Nijar ta yiwa Masar bazata
  Tawagar Pharaohs wacce take ta tara a duniya ta kasa doke Nijar wacce Fifa tace ita ce ta 154 a duniya. Abin da ya zowa masu sharhi a fagen kwallon kafa da bazata.
 • Nijar ta yiwa Masar bazata
  A halin yanzu dai bayan karawa biyua rukunin G, Nijar na da maki uku a yayinda Masar keda maki guda. Sai a watan Maris na badi Nijar za ta hadu da Sierra Leone a wasanta na gaba
 • Nijar ta yiwa Masar bazata
  Dubban 'yan kasar ne suka bazu kan tituna domin nuna farin cikinsu da nasarar da kasar ta samu jim kadan bayan kammala wasan, inda suka yi ta kade-kade da raye-raye.

BBC navigation

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.