An sabunta: 8 ga Disamba, 2010 - An wallafa a 11:00 GMT

Taron shugabannin kungiyar Ecowas a Abuja

  • Shugabannin kungiyar habaka tattalin arzikin kasashen Yammacin Afrika wato ECOWAS ko CEDEAO sun dakatar da kasar Ivory Coast saboda da rikicin shugabanci da kasar ta shiga.
  • Shugabannin wanda suka gudanar da taro a babban birnin Najeriya, Abuja sun tabbatar da Alassane Ouattara a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar.
  • Shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya wanda ya bayyana matsayin kungiyar bayan sun kammala taron ya bukaci shugaba Laurent Gbagbo da ya yi murabus.
  • A yanzu dai duka mutanen biyu, wato Laurent Gbagbo da Alassane Ouattara sun fara yunkurin kafa gwamnati.
  • Majalisar dinkin duniya da kasar Faransa da Tarayyar Afrika sun yi kira ga Mista Gbagbo da yayi murabus, amma kawo yanzu bai nuna alamar yin hakan ba.
  • Bayanai sun nuna cewa a yanzu ana fama da karancin kayan masarufi a kasar Ivory Coast, yayinda farashin wasu kayayyakin ciki har da Cocoa ya tashi, yayinda ake ci gaba da fama da kiki-kakan siyasa.
  • Shaguna da dama sun rufe saboda karancin kayayyaki da suka hadar da nama, kifi, fetur, iskar gas din girki da sauransu.

BBC navigation

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.