An sabunta: 7 ga Disamba, 2010 - An wallafa a 14:39 GMT

Zanga-zanga a kasar Ivory Coast

  • Bayanai sun nuna cewa a yanzu ana fama da karancin kayan masarufi a kasar Ivory Coast, yayinda farashin wasu kayayyakin ciki har da Cocoa ya tashi, yayinda ake ci gaba da fama da kiki-kakan siyasa.
  • Shaguna da dama sun rufe saboda karancin kayayyaki da suka hadar da nama, kifi, fetur, iskar gas din girki da sauransu.
  • Kasar ivory Coast dai ita ce kasar da ta fi kowacce samar da Cocoa a duniya.
  • Yayinda ake ci gaba da zaman dar-dar a kasar, majalisar dinkin duniya ta fara janye ma'aikatanta da aikinsu bai zama dole ba daga kasar.
  • A ranar Litinin mai shiga tsakani na tarayyar turai, tsohon shugaban Afrika ta Kudu Thabo Mbeki ya bar kasar ta Ivory Coast bayan tattaunawar da ya gudanar da bangarorin biyu ya kasa kawo karshen rikicin.
  • Kasar ta Ivory Coast dai ta rabu biyu tun shekarar 2002 sakamakon yakin basasa.
  • A baya dai ana ganin kasar a matsayin watta aljannar zaman lafiya a yammacin Afrika.

BBC navigation

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.