An sabunta: 14 ga Disamba, 2010 - An wallafa a 13:52 GMT

Zanga-zanga a Majalisar Dokokin Najeriya

  • A Najeriya, wasu matasa dake zanga-zanga sun mamaye kofar shiga ginin Majalisun dokokin kasar.
  • Masu zanga-zangar wadanda suke dauke da kwalaye sun taru a gaban Majalisar ne domin nuna adawa da shirin da majalisun kasar ke yi na amince wa da wani sashi na dokar zabe.
  • Dokar zai ba su damar kasancewa mambobi a kwamitin zartarwa na jam'iyyunsu.
  • Masu zanga-zangar wadanda ke dauke da kwalayen da ke Allah wadai da kudurin da ke son baiwa 'yan majalisa damar zamowa mambobi a kwamitin zartarwa na jam'iyyunsu, sun kasa sun tsare bakin kofar shiga majalisar.
  • A bangare guda jami'an tsaro sun yi gadin ginin majalisar da kuma tabbatar da hana barkewar rikici a kofar majalisar
  • Jami'an tsaron dai sun girke wata babbar mota dauke da wata bindiga mai sarrafa kanta a kofar shiga majalisar
  • Sai dai a yayin da wadanda suka shirya zanga-zangar ke cewa suna son kare hakkinsu, a gefe guda wadansu matasa na kokawa kan kudin mota ne.

BBC navigation

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.