Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Tattaunawa ta musamman kan bikin kirsimeti

A yayinda mabiya addinin kirista a sasa daban daban na duniya ke gudanar da bukukuwan Kirsimeti domin tunawa da ranar haihuwar Annabi Isa Almasihu.

Sai dai ba dukkan kiristoci ne suka amince da wannan ranar ta ashirin da biyar ga watan disamba a matsayin ranar da aka haifi Yesun ba, a don haka akwai wadanda ba sa bukukuwan a ranar.

A lokacin bukukuwan dai wasu mabiya addinin Kiristan kan gudanar da wasu halaye da dabi'u na masha'a da sunnan bukukuwan Kirsimeti. Ko hakan na da asali? Wadannan na daga cikin batutuwan da Bashir Sa'ad Abdullahi ya yi wata tattaunawa ta musamman a kansu tare da wasu limaman addinin kirista a Abuja. A yi sauraro lafiya.