An sabunta: 24 ga Janairu, 2011 - An wallafa a 17:50 GMT

Hotuna: Harin bam a filin saukar jiragen sama a Moscow

  • Rahotanni daga babban birnin Rasha, Moscow na nuni da cewa an samu fashewar Bam a filin saukan jiragen sama na Domodedovo, inda ake kyautata cewa mutane 31 sun mutu sanadiyar fashwar bam din.
  • Har wau yau rahotanni na cewa mutane 100 sun jikkata sanadiyar harin wanda aka ganin dan kunnar bakin wake ne ya fasa bam din.
  • Babban mai bincike na kasar Rasha ya ce 'yan ta'ada ne su ka kai harin, a yayinda shi kuma shugaban kasar Dmitry Medvedev ya ce kasar za ta tabbatarda kama wadanda suka gudanarda harin.
  • Filin saukan jiragen saman na wajen kilomita 40 daga cikin garin na Moscow.
  • A kodayaushe dai filin saukar jiragen saman na cike da baki daga kasashen waje da kuma masu yawon bude ido.
  • 'Yan sanda sun tsaurara matakan tsaro a filayen jiragen saman dake fadin kasar.

BBC navigation

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.