Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Haifi ki yayaye da BBC Hausa: Awon farko

Masu iya magana dai na cewa kyaun alkawari cikawa. To idan masu sauraro za su iya tunawa, Malama Amina Musa ita ce mace mai karamin ciki da wannan shiri ya fara bi don ganin yadda take goyon ciki da laulayi.

To cikin yardar Allah ga shi yanzu cikinta ya kai wata na hudu, kuma kamar yadda mukayi alkawari, wakiliyar BBC a Maiduguri Bilkisu Babangida ta yi wa malama Amina rakiya zuwa asibiti don gane ma idonta, abinda ke faruwa a wajen awon farko ga dai yadda ta kasance.

To Muhimmancin zuwa awo ga mace mai juna biyu dai ba ya misaltuwa, musamman wajen rage hadarin da a wasu lokutan kan kai ga mace-macen mata masu juna biyu da kuma jariransu.

Sai dai a arewacin Najeriya, yankin da akafi samun yawaitar mace-macen mata masu juna biyu a kasar, ba ta sauya zani ba domin yankin shi ne koma baya wajen yawan matan dake zuwa awon ciki tare da samun cikakken kulawa daga kwararrun ma'aikatan lafiya.

Wani binciken da akayi a shekarar 2008, wanda hukumar kidaya ta Najeriya ta yi da tallafin hukumar raya kasashe masu tasowa ta Amurka USAIDS da hukumar kula da al'umma ta majlisar dinkin duniya UNFPA kan lafiyar' al'ummar kasar tare da yin la'akari da shekaru da jinsin su ya duba yawan mata masu juna biyu dake samun kyakkyawar kulawa daga kwararrun ma'aikatan lafiya a kasar.

Shirin mu kenan na wannan makon, kuma ayi sauraro lafiya.