Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Haifi ki yaye da BBC Hausa: Kula da mace mai juna biyu

A karkashin tsarin kiwon lafiya a Biutaniya wato NHS akwai jerin kwarrarun ma'aikatan lafiya da ke ba da kulawa ga mata masu juna biyu har bayan haihuwa.

Wadannan ma'aikata sun hada da unguwar zoma wadanda suke da kwarewa kan abinda ya shafi goyon ciki da haihuwa kuma ana samunsu a asibitoci ko kuma a cikin al'umma, sannan sai likitan unguwa wato GP, sai kuma likita dake da kwarewa ta musamman akan kulawa ga mace mai ciki, sai likitan yara da kuma ma'aikatan jiyya wato nas-nas.

To masu iya magana dai na cewa waka ta fi dadi a bakin mai ita, hakan ya sa daga London Aichatou Moussa ta tuntubi wata mai ciki dake zaune a Newcastle a Ingila, Hajiya Fatima don jin yadda mata masu juna biyu ke samun kulawa a can.

To game da wannan batu na rashin bada kyakkyawar kulawa da ake zargin wasu ma'iakan lafiya na yi ga mata masu juna biyu ya sa muka nufi Najeriyar, inda wakilin BBC a jihar kano Yusuf Ibrahim Yakasai ya duba mana yadda lamarin yake musamman a wasu asibitocin gwamnati inda lamarin ya fi kamarai.

A Sokoto garin Shehu ko ya lamarin yake? Wakilin BBC a can Haruna Shehu Tangaza shi ma ya duba mana wannan batu.

Daga Najeriya za mu nufi makociyar kasar wato jamhuriyyar Nijar, kamar yadda za ku ji a rahoton Tchima Illa Issoufou, rashin bada kyakkaywar kulawa ga mata masu juna biyu na cigaba da hana wasu matan zuwa awo. Shirin kenan na wannan makon, sai ayi sauraro lafiya.