Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Haifi kiyaye da BBC Hausa: Karbar haihuwa a karkara

Hakkin mallakar hoto google

Hadaddiyar kungiyar ungozoma ta kasa da kasa ICM ta bayyana ungozoma a matsayin macen da ta samu ilimin zamani daga cibiyar bada ilimin da aka amince da ita a kasar da take, kuma ta samu nasarar kammala karunta akan karbar haihuwa kuma take da lasisi a hukunce na yin wannan aiki na ungozoma. To ta kowace fuska ka kalli karbar haihuwa kasan ba abu bane kawai da a dare daya mutum zai fada yinsa, musamman idan haihuwar ta zo da gardama.

Sai dai a halin da muke ciki hatta unguwar zoman dake da ilimin karbar haihuwa na zamani da ake da su a duniya sunyi karanci, idan aka kwatanta da yawan mata masu ciki dake bukatar kulawarsu a duniya.

Wani rahoto da hukumar lafiya ta duniya ta wallafa a shekarar 2005 yace ana bukatar karin uguwar zoma 334,000 a duniya, don rage yawan mace-macen mata masu juna biyu da mutuwar jarirai, ko rage abubuwan dake janyo musu nakasa.

Hadaddiyar kungiyar ta ungozoma dake da kungoyoyin ungozoma 99 a kasashe 88 na duniya ta bayyana cewa samun kulawa a hannun kwarraru ga mace mai juna biyu da kuma lokacin da tazo haihuwa hakki ne da ya zama dole a bata. Inda ta jaddada cewa a fadin duniya ana bukatar sanya kudade don horar da ungozoma.

Kungiyar dai ta kuma ambato tsohuwar shugabar hukumar kula da al'umma ta majalisar dinkin duniya, Thorayya Obaid na cewa samun kwararrun ungozoma na da muhimmancin gaske wajen haihuwa lafiya, saboda haka yakamata kowace mai ciki ta samu kulawa daga ungozoma.

Shirin mu kenan na wannan makon. Ayi sauraro lafiya.