An sabunta: 4 ga Aprilu, 2011 - An wallafa a 13:03 GMT

Hotuna: Ana ci gaba da fafatawa a Ivory Coast

Hotuna: Ana ci gaba da fafatawa a Ivory Coast

 • Hotuna: Ana ci gaba da fafatawa a Ivory Coast
  Dakarun dake biyayya ga mutumin da kasashen duniya suka ce shi ya lashe zaben shugabancin kasar Ivory Coast, Alassane Ouattara, sun taru a wajen birnin Abidjan ranar Lahadi.
 • Hotuna: Ana ci gaba da fafatawa a Ivory Coast
  Wani mayaki da ke goyon bayan Alassane Ouattara yana bayyana abubuwan yaki na gargajiya a daidai lokacin da sojojin ke taruwa a wajen birnin Abidjan.
 • Hotuna: Ana ci gaba da fafatawa a Ivory Coast
  Wani hoto da Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta fitar, na nuna wata mata dauke da kayanta aka, tana kan hanya tare da 'yarta, inda suka nufi garin Zwedru kusa da Tchien a Kudancin Liberia a ranar 24 ga watan Maris, 2011.
 • Hotuna: Ana ci gaba da fafatawa a Ivory Coast
  Wata tankar yaki ta sojojin Faransa na tafiya a kan titi, a daidai lokacin da sojojin Faransar ke ci gaba da sunturi a birnin Abidjan a ranar 2 ga watan Afrilu, 2011.
 • Hotuna: Ana ci gaba da fafatawa a Ivory Coast
  Dakarun da ke goyon bayan Laurent Gbagbo suna gadin fadar shugaban kasa, wacce ke karkashin ikonsu a Abidjan. Alassane Ouattara ya yi watsi da zargin cewa dakarunsa sun aikata kisan gilla.
 • Hotuna: Ana ci gaba da fafatawa a Ivory Coast
  Wasu fararen hula sun daga hannayensu sama a daidai lokacin da suke wuce wa ta gaban wani sojo da ke goyon bayan Laurent Gbagbon a birnin Abidjan.

BBC navigation

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.