An sabunta: 6 ga Aprilu, 2011 - An wallafa a 12:50 GMT

Hotuna: Ana kai hari gidan Gbagbo

  • Shugaban kasar Ivory Coast Laurent Gbagbo wanda yake buya a karkashin fadarsa ta shugaban kasa, ya ki sauka daga kan karagar mulki.
  • Dakarun dake biyayya ga abokin hamayyarsa Alassane Ouattara su yi kawanya a gidansa da ya zaune kuma suna kai hari.
  • Mista Gbagbo ya shaidawa gidan talabijin na kasar Faransa cewa ya amince da tattaunawa tare da Mista Ouattara, kuma ya yarda a sake kidaya kuri'un zabenda aka gudanar a watan Nuwambar bara, amma yace ba zai mika wuya ba.
  • Wakilin BBC ya ce watakila abinda Mista Gbagbo ke so shine wata kasar da za ta karbe shi.
  • To sai dai a baya bangaren Mista Ouatarra sun yi kira da a gurfanar da Laurent Gbagbo a gaban kuliya, saboda laifukan yaki da suke zarginsa da aikatawa.

BBC navigation

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.