Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayi Riga: Amfani da kudi wajen siyan kuri'u

Image caption Ana dai samu masu siyarda kuri'unsu duk da irin matsanancin rayuwar da suke fuskanta

Zargin batun sayen masu zabe ta amfani da kudi, da tufafi da sabulu da kayan abinci da sauran kayan jan hankali dai batu ne da aka dade ana korafi kan sa a cikin tsarin zaben Najeriya.

Koda a zaben yan majalisar dokoki na kasa da aka yi ranar asabar din da ta gabata wannan batu ya fito karara. Ana kuma zargin cewar galibin kudin da kuma abubuwan jan hakalin jama'ar suna kuma fitowa ne daga baitul malin Gwamnati - wato kudade ne na jama'a da ya kamata a ce an yi masu ayyukan more rayuwa . Kuma an yi zargin cewar ana yin wannan abu ne a kan idon wadanda aka dora wa alhakin tabbatar da ganin an yi zaben cikin tsarin gaskiya da adalci da kuma tabbatar da kariyar masu zaben da jami'ansa - wato jami'an tsaro.

A wasu wurare dai wannan al'amari kan haifar da rikici a lokacin zabe.To Shin, yaya za a yi maganin irin wannan matsala a lokacin sauran zabukan da ke tafe? A kan haka ne zamu tattauna a filin Ra'ayi Riga na yau. Mun gayyato baki da za su shiga cikin wannan shiri daga cikinsu kuwa akwai Alh Mamman Tsafe, Kwamishinan Yansanda na Jihar Kwara da Alh Faruk Iya, Shugaban Jam'iyyar PDP a Jihar Kano da Dr Usman Bugaje, Dan takarar Gwamna na jama'iyar ACN a Jihar Katsina da,Dr Mohammed Sani Bello (Mainan Zazzau) Babban Daraktan yakin neman zaben Dan takarar Shugaban kasa a Jama'iyar ANPP, Malam Ibrahim Shekarau da kuma Mr Nick Dazang Mataimakin Darakta mai kula da hulda da jama'a da Yada Labarai na Hukumar zabe ta Najeriya INEC .

Akwai kuma wasu daga cikinku, Ku masu saurarenmu da za su kansance kan layin wayar tarho. Ayi sauraro lafiya.