An sabunta: 8 ga Yuni, 2011 - An wallafa a 16:51 GMT

Najeriya cikin hotuna: 8/9 ga watan Juni 2011

Najeriya cikin hotuna: 8/9 ga watan Juni 2011

 • Najeriya cikin hotuna: 8/9 ga watan Juni 2011
  Daya daga cikin wuraren da aka kai harin bom a jihar Borno dake Arewacin Najeriya, inda mutane biyar ne suka rasu yayinda da dama suka samu munanan raunuka. Bilkisu Babangida ce ta dauko hotuna
 • Najeriya cikin hotuna: 8/9 ga watan Juni 2011
  Daya daga cikin bama-baman ya fashe ne kusa da Caji Ofis na Dandal dake tsakiyar birnin Maiduguri.
 • Najeriya cikin hotuna: 8/9 ga watan Juni 2011
  Bom ya kuma daidaita wani bututun ruwa a kusa da ofishin 'yan sandan na Dandal.
 • Najeriya cikin hotuna: 8/9 ga watan Juni 2011
  Hukumar tabbatarda ingancin abinci da magungunan ta Najeriya, NAFDAC, ta lalata ton-ton na jabun magunguna da ta kama a cikin shekara dayan da ta gabata a jahar Sakkwato. Haruna Tangaza ne ya dauko hotuna
 • Najeriya cikin hotuna: 8/9 ga watan Juni 2011
  Bayanai sun nuna cewar Najeriyar dai ita ce kasuwa mafi girma ta jabun magunguna da yawanci ake harhadawa a kasashen Indiya da China da kuma kasar kanta.
 • Najeriya cikin hotuna: 8/9 ga watan Juni 2011
  Binciken Hukumar Lafiya ta duniya dai ya nuna cewar, tsakanin kashi 30 zuwa sittin cikin dari, na magunguna a Nahiyar Afrika na jabu ne, ko kuma marasa inganci.

BBC navigation

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.