Hotuna: Sabuwar kasar Kudancin Sudan

A ranar Asabar 9 ga watan Yuli, Kudancin Sudan zai zamo kasa mai cin gashinta, bayan kuri'ar raba-gardamar da basu damar ballewa daga Arewacin Sudan.

Sabuwar kasar Kudancin Sudan
Bayanan hoto,

A ranar Asabar 9 ga watan Yuli, Kudancin Sudan zai zamo kasa mai cin gashinta, bayan kuri'ar raba-gardamar da basu damar ballewa daga Arewacin Sudan.

Bayanan hoto,

Wannan dai na cikin wani bangare na yarjejeniyar zaman lafiyar da aka cimma a shekara ta 2005 bayan shafe shekaru 21 ana gwabza kazamin fada tsakanin bangarorin biyu wanda ya yi sanadiyyar mutuwaer mutane kusan miliyan biyu.

Bayanan hoto,

Akwai dai babban kalubale a gaban sabuwar kasar wacce ita ce mafi karancin shekaru a nahiyar Afrika - ganin yadda ake fama da rashin tsaro ga kuma mummunan talauci.

Bayanan hoto,

Ana zargin shugabanninta da cin hanci da rashawa da kuma take hakkin bil'adama - wanda ake ganin zai kawo wa kasar koma baya.

Bayanan hoto,

Yawancin mazauna yankin na fama da mummunan talauci ga kuma rashin tsaron da ya addabi yankin. A yanzu haka gwamnatin yankin na fada da kungiyoyin 'yan tawayen kusan bakwai

Bayanan hoto,

Kudancin Sudan na cike ne da daji da kuma fadama, a yayinda kuma Arewacin kasar ke cike da sahara.

Bayanan hoto,

Yawancin mazauna Arewacin kasar na magana ne da harshen Larabci kuma yawancisu musulmai ne, shi kuma yankin kudancin kasar na tattare ne da kabilu daban-daban wadanda yawancinsu mabiya addinin kirista ne da kuma mabiya addinin gargajiya.

Bayanan hoto,

Fadan da aka shafe shekaru 21 ana gwabzawa ya yi sanadiyyar mutuwar mutane miliyan biyu tare da jefa wasu miliyoyin zuwa gudun hijira