An sabunta: 21 ga Yuli, 2011 - An wallafa a 13:40 GMT

Zanga-zangar kin jinin gwamnati a Malawi

  • Shugaban kasar Malawi, Bingu wa Mutharika, ya ki ya sauka daga mulki duk da cewa akalla mutane takwas sun rasa rayukansu a zanga zangar kin jinin gwamnati da aka kwashe kwanaki biyu ana yi.

  • A jawabin da yaiwa kasar, shugaba Mutharika ya ce ba wata matsala da za'a warware da tashin hankali, kuma zai yi magana da 'yan adawa.

  • Ya ce a shirye yake yanzu fiye da ko yaushe na a tattauna.

  • Ya kuma yi kira ga 'yan adawa da shugabannin fararen hula dake kuka da gwamnati da su zo a zauna a tattauna.

  • Rikicin dai ya fara ne kan haushin lakadawa wasu masu fafutukar kare hakkin bil adama da 'yan jarida duka.

BBC navigation

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.