Bikin Karamar Sallah a jihar Kano

A ranar Talace musulmai a fadin duniya su ka gudanar da bukukuwan karamar sallah bayan kammala azumin watan Ramalana.

A ranar Talace musulmai a fadin duniya su ka  gudanar da bukukuwan karamar sallah bayan kammala azumin watan Ramalana.
Bayanan hoto,

A ranar Talace musulmai a fadin duniya su ka gudanar da bukukuwan karamar sallah bayan kammala azumin watan Ramalana.

Bayanan hoto,

Daruruwar musulmai ne su ka halarci sallar idi a masallacin idin kofar mata

Bayanan hoto,

Bukukuwa da dama ne dai ke biyo bayan sallar da aka gudanar da sanyin safiya.

Bayanan hoto,

A lokotan bukukuwan sallar dai jama'a kan ziyarci yan uwa da abokan arzuka tare da raba abinci na gargajiya nau'i nau'i dan taya juna murnar sallar.

Bayanan hoto,

A Kasar hausa dai hawan sarki shine mafi girma a cikin bukukuwan sallah, inda sarki da hakimansa ke hawa dawaki cikin shiga ta gargajiya tare da kewaya gari dan ganawa da jama'a.

Bayanan hoto,

Gwamantin Jihar kano a bana tace babu hawan da za'ayi saboda rashin lafiyar sarkin Kanon.

Bayanan hoto,

Jama'a sun taru na cin abinci bayan sun sauko daga sallar Idi

Bayanan hoto,

Yara sun taru a kofar gidan Zoo, inda su ka kawo ziyara.