An sabunta: 26 ga Oktoba, 2011 - An wallafa a 08:50 GMT

An yi fata-fata da mahaifar Kanal Gaddafi

Garmaho

Mazauna garin Sirte mahaifar tsohon shugaban Libya Kanal Gaddafi, sun fara komawa gida bayan yakin da aka gwabza a garin.

Sai dai fatansu na komawa gidajensu ya dusashe bayan da suka tarar an yi fata-fata da gidajen na su tare da sace kayayyakin da ke ciki.

A gefe guda kuma, an gano gawarwakin wasu magoya bayan Kanal Gaddafin a wani otel a garin na Sirte bayan an karkashe su, a cewar kungiyar kare hakkin bil'adama ta Human Rights Watch.

Sabbin mahukuntan kasar ta Libya dai sun musanta hannu a ta'asar.

BBC navigation

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.