An kashe fararen hula a Somalia

Hakkin mallakar hoto other
Image caption Makwanni biyu kenan da Kenya ta shiga Somalia domin yakar kungiyar al-shabaab

Kungiyar bada agaji ta Medecins Sans Frontieres ta ce akalla mutane uku sun mutu a yayinda sama da hamsin su ka jikkata a wani harin ta sama da kasar Kenya ta kai a Somalia.

Kungiyar ta ce yawancin wadanda harin ya shafa mata ne da yara.

Kenya dai ta ce ta kaddamar da harin ne akan kungiyar nan mai kishin Islama ta al-Shabaab.

Kungiyar bada agaji ta Medecins sans Frontieres dai ta ce an kai hari ne a wani sansani na 'yan gudun hijira da ke Jilib a kudancin Somalia.

Wani mai magana da yawun sojin Kenya ya ce masu tada kayar baya goma sun mutu a harin a yayinda guda arba'in da bakwai su ka jikkata.

Ya musanta rahotannin da ke nuni da cewa harin da kasar ta kaddamar ya shafi fararen hula, inda ya ce duk farfaganda ce ta kungiyar al shabaab.

A yanzu haka dai makwanni biyu kenan da Kenya ta tura sojojinta cikin Somalia, bayan an samu rahotanin sace sacen bakin kasashen waje a Kenya,wanda kuma kasar ta daura alhakin hakan akan kungiyar al shabaab.