Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Amsoshin Takardunku 05/11/2011

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Niamey

An haifi tsohon shugaban Niger, Janar Ali Saibou ne a garin Dingazy Banda da ke jihar Tillaberi, a shekarar 1940. Ya rike mukamin shugaban kasa, bayan mutuwar Janar Seini Kountche.

A karkashin mulkin Janar Ali Saibou ne aka gudanar da babban taron kasa na Conference Nationale a shekarar 1991.

Janar Ali Saibou ya gudanar da zaben farko na jam'iyyu barkatai, inda ya mika mulki ga Malam Mahaman Ousmane a 1993.

Hakkin mallakar hoto BBC World Service

Haka nan kuma shirinmu yana kunshe da cikakken bayani akan hawan Arafat.

Hawan dutsen Arafat dai shine kololuwar aikin Hajji, kuma wajibi ne ga duk wani mai aikin Hajji.

Mutane fiye da miliyan biyu ne suke aikin hajjin a wannan shekarar.