Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Haifi ki yaye da BBC Hausa: Al'adar yaye a wasu birane

Hakkin mallakar hoto RIA Novosti

A wannan makon ma zamu duba al'adar yaye a wasu biranen. In baku manta ba a makon da ya gabata mun duba al'adar yaye a kauye.

A baya mun fassara yaye kamar yadda sashen lafiya na BBC da Hukumar lafiya ta Birtaniya suka ce, a matsayin wani mataki na fara janye yaro daga shan nono ta hanyar koya masa cin wasu nau'in abincin domin ya saba dasu kafin lokacin da zai daina shan nono kwata kwata.

To amma ma'anar yaye a kasar Hausa na nufin janye yaro daga shan nonon baki daya.

Babban dalilin da aka yadda dashi cewa ya kamata a yaye yaro shine domin ya kai matakin girma.