Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayi Riga: Magance rikicin jihar Kaduna

Hakkin mallakar hoto b
Image caption Wasu da rikicin addini ya shafa a Najeriya

Najeriya dai ta jima tana fama da rikicin addini da na kabilanci, musamman ma a yankin Arewacin kasar, wanda ya haddasa asarar dimbin rayuka da dukiya.

Daya daga cikin yankunan da aka sha fama da irin wadannan rikice-rikice a shekarun baya, ita ce jihar Kaduna.

Amma a farkon shekara ta 2000, gwamnati da kungiyoyi daban-daban sun tashi tsaye wajen shawo kan matsalar.

Sai dai da alama a 'yan watannin nan, matsalar na neman sake kunno kai, inda daruruwan mutane suka rasa rayukansu, a rikicin da ya biyo bayan zaben shugaban kasa na watan Afrilun da ya gabata.

A makon jiya ma, wasu mahara sun hallaka wasu mata 2, tare da raunata wasu mutane 14, a wani Coci da ke garin Zonkwa, a karamar Hukumar Zangon Kataf.

Rikici na baya-bayan nan da aka yi, ya faru ne a garin Kafanchan, tsakanin matasa Musulmi da Kirista, bayan kisan wani dan Achaba musulmi.