Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Cigaban Demokradiyya da tattalin arziki a Afrika

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Masu zanga-zanga na artabu da 'yan sanda a Kinshasa

A 'yan shekarun nan dai, wani muhimmin batu da ke jan hankalin jamaar Afrika shi ne na yadda zaa bunkasa tsarin Demokradiyya da kuma tattalin arzikin kasashen nahiyar.

Masu nazari kan harkokin siyasa dai na ganin cewa akwai matsaloli da dama da ke kawo tarnaki wajen bunkasa Demokradiyya da cigaban tattalin arziki a kasashen na Afrika.

Matsalolin sun hada da rashin gudanar zabe sahihi, da cin hanci da rashawa da rashin shugabancin na gari.

A kwanan nan, Hukumar Guildhall ta birnin London ta shirya wani taro inda ta gayyaci kwararru daban daban don tattaunawa a kan batun na Demokradiyya da tattalin arziki a kasashen na Afrika.

Daya daga cikin wadanda suka gabatar da lacca a wurin taron, shi ne Dr Jibrin Ibrahim, shugaban Cibiyar raya Demokradiyya dake Abuja. Ya kawo mana ziyara sashen Hausa, kuma Sulaiman Ibrahim ya tambaye shi ko zaa iya cewa an samu cigaba a Afrika a fannin na Demokradiyya da tattalin arziki?