Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Cikakken bayani a kan shirin janye tallafin mai a Najeriya

Hakkin mallakar hoto b
Image caption wasu masu shan mai a Lagos

A cikin Filin Amsoshin Takardunku na wannan makon, za ku ji cikakken bayani daga bakin Farfesa Murtala Sagagi na jami'ar Bayero dake Kano a kan shirin gwamnatin Najeriya na janye tallafin man fetur da kuma wasu matakai da ake ganin za su taimaka wajen kyautata al'ammura, ba tare da cire tallafin ba.

Hakazalika za ku ji Elhadji Diori Coulibaly yana yin karin bayani a kan sabon shafin Intanet na sashen Hausa na BBC, wanda muka kaddamar a ranar 17 ga watan Nuwamba.

Ahmed Abba Abdullahi ne ya gabatar da Filin.