Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Garin masoyi ba ya da nisa

Image caption Mr Dolego

A cikin filin Taba Kidi Taba Karatu na wannan makon, za ku ji labarin wani tsohon dan takarar gwamna a Amurka, wanda ya je neman wata budurwarsa zuwa Ukraine, amma bai gan ta ba, wanda hakan ya jefa shi cikin wani mawuyacin hali.

Mr Dolego dai ya hadu da maatar mai suna Yulia ta hanyar intanet inda har suka rika yin musayar bayanai da hotuna, amma da ya je Ukraine din sai Yulia din ta yi shashataw, ta yi kasa ko sama.

Mr Dolego dai ya shafe kwanaki da dama ba tare da ganin Yulia ba, har ya kai kudinsa suka kare, ya rika kwana a waje.

A karshe dai har ya kwanta a asibiti, amma duk da wannan mawuyacin halin da ya shiga, Mr Dolego ya ce ba zai koma gida ba, sai ya ga Yulia da idonsa.