Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayi Riga: Rundunonin 'yan sanda na jihohi

Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan, ya ce lokaci bai yi ba da za a baiwa jihohin kasar izinin kafa rundunoninsu na 'yan sanda.

Ya bayyana hakan ne a lokacin taron shiyyar arewa ta tsakiya na Majalisar Fahimtar Juna Tsakanin Mabiya Addinai, wanda aka yi a birnin Ilori na Jihar Kwara.

A cewar shugaban, akwai matukar yiwuwar a yi amfani da rundunonin 'yan sandan jihohin ta hanyar da ba ta dace ba, saboda yanayin siyasar da ake ciki.

Sai dai Majalisar Dattawan Najeriyar, da ma wadansu gwamnonin jihohi, su na bukatar gwamnati ta baiwa jihohin damar kafa rundunoninsu na yan sanda, domin tafiyar da sha'anin tsaro.

Wannan shi ne batun da za a tattauna a kai a filin Ra'ayin Riga.