Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Matsalar karancin wutar lantarki a Najeriya

Hakkin mallakar hoto bbc
Image caption Layukan wutar lantarki a Najeriya

A daidai lokacin da wa'adin da gwamnatin Najeriya ta deba na shiga cikin jerin kasashen duniya ashirin da suka fi karfin tattalin arziki ke kara matsowa, har yanzu ana cigaba da fuskantar matsalar karancin wutar lantarki a kasar.

Wadatar wutar lantarkin dai na daga cikin manyan ginshikan samun cigaba tattalin arziki.

Wannan dai na zuwa ne duk da matakai daban-daban da gwamnatin Najeriyar ke cewa tana dauka na yiwa sashen samar da wutar lantarkin garambawaul da zummar gano bakin zaren matsalar da kuma samar da wadatacciyar wutar lantarki a kasar.

Wakilinmu a Sakkwato Haruna Shehu Tangaza ya duba mana wannan batun ga kuma rahoton na musamman da ya shirya mana kan karancin wutar lantarki a Najeriyar.