Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ko za a samu bore irin na kasashen Larabawa a Afrika?

A daidai lokacin da ake bukukuwan tunawa da boren da aka yi a kasashen Tunisia da Masar wanda ya kifar da gwamnatocin kasar, sannan ya haifar da bore a wasu kasashen Larabawa.

Tambayar ita ce ko za a sami makamancin wannan boren a kasashen Afrika?

Yan Najeriya da dama ne ke amfani da hanyoyin sadarwa na zamani wajen gudanar da zanga-zanga domin nuna adawa da wasu matakan da gwamnatin kasar ke dauka.

Irin wadannan mutane sun fito daga bangarori daban-daban na kasar, kuma sun shaida wa Ibrahim Shehu Adamu a Abuja cewa, boren na kasashen Larabawa ya yi tasiri wurin yunkurin na su: