Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Fashewar rumbun makamai a Tarayyar Congo

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Wasu daga cikin mutanen da ake jinyarsu

Hukumomi a Tarayyar Congo sun nemi taimakon kasashen duniya bayan da fashewar wasu abubuwa a wani rumbun ajiyar makamai ya hallaka kusan mutane dari biyu da hamsin.

Jami'ai sun ce kusan mutane dubu daya da dari biyar ne suka jikkata sakamkon fashewar a babban birnin kasar, Brazaville.

Har yanzu masu aikin ceto na ci gaba da neman wadanda suka tsira da rayukansu yayinda ake faragabar yawan wadanda suka rsa rayukansu zai karu.