Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

An kame wasu masu satar bayanai ta intanet

Hakkin mallakar hoto BBC World Service

An kame wadansu mutane bakwai a lokaci guda a Amurka da Burtaniya da kuma Jamhuriyar Ireland, wadanda aka tuhuma da satar bayanai ta intanet.

Hukumar bincike ta FBI a Amurka ta ce mutanen mambobi ne a kungiyar LulzSec, wacce ake kyautata zaton shugabanta, Monsegur, ya zamo karan farautar 'yan sanda.

Takardun kotu sun bayyana cewa Monsegur babban mai fada aji ne a wadansu kungiyoyi uku na masu satar bayanai wadanda suka hada da Internet Feds da Lulz Security - wadanda aka dorawa alhakin satar bayanan kamfanoni da kuma gwamnatoci a sassan duniya daban-daban.