Labarai cikin hotuna

Wasu daga cikin labarruka daga sassa daba- daban na duniya a cikin hotuna.

Games athletetics
Bayanan hoto,

Alexis Copello dan kasar Cuba ya fada kan yashi a lokacin wasan tsalen badaken uku na maza a wasanin dake gudana a Atakoy dake birnin Santanbul a Turkiya.

Bayanan hoto,

Dakarun Amurka a Afghanistan sun kasance cikin shirin ko ta kwana sakamakon kisan da wani sojan Amurka yayiwa wasu fara hula su goma sha shidda a Afghanistan. Jami'an Amurka sunyi gargadin zaa fuskanci ramuwar gaya bayan harin da sojan ya kaiwa wasu kauyuka kusa da wani sansanin soji a Kandahar. Yara kanana tara na cikin wadanda aka kashe

Bayanan hoto,

Wasu mutane sun zauna kusa da bakin tekun dake kudu maso gabashin birnin Nice a Faransa

Bayanan hoto,

Japan ta gudanar da bikin tunawada girgizar kasa da tsunami da suka afkawa yankin Arewa maso gabashin kasar inda mutane akalla dubu ashirin sun hallaka ko sun bace. Girgizar kasa me karfin marki 9.0 ta auku ne sakamakon hadarin da ya faru a tashar nukiliya ta Fukushima

Bayanan hoto,

Wani matuki na kokarin tada kumbo na balan -balan a bikin Canbera a kasar Australia |

Bayanan hoto,

Dan kasar Indonesia Umar Patek da ake zargi da hada bam ya daga hanu ga manema labaru a lokacin da ya isa wata kotu a yammacin Jakarta gabanin shariarsa. Ana tuhumarsa da aikata laifuka shidda ciki harda da kisa , hada bama bamai da kuma mallakar makamai ta haramtaciyyar hanya game da hare haren da aka kaiwa wani gidan disco a shekerar 2002

Bayanan hoto,

Wata yar Tibet ta rike tutar Tibet a lokacin da aka yi wata zanga zanga a Delhi dake India a ranar bikin tunawa da boren da mata yan Tibet suka yi.

Bayanan hoto,

Ayarin dawakai da suka samu horaswa daga wurin Willie Mullins na astseye gabanin gasar sukuwar da zaa yi Cheltenham a Ingila