Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayi Riga: Yaya za a kawo karshen cin zarafin kananan yara?

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Masu zanga-zanga na kiran a kare 'yancin yara

Kungiyoyin agazawa yara na duniya sun ce matsalar cin zarafin kananan yara ta hanyar lalata da su tana kara yawaita a kasashen Afrika.

Ko da yake a cewar wasu gwamnatocin kasashe musamman na yammacin Afrika, an samu raguwar wannan matsala sakamakon tsauraran matakan da suka ce sun dauka.

A cewar kungiyoyin kare hakkin kananan yara, ba a fiya aiki da dokar hukunta wanda ya ci zarafin yara musamman ta hanyar lalata ba a yawancin kasashe, inda akan fifita masu hannu da shuni ko masu fada a ji a kasa a maimakon wadanda aka ci zarafin na su, wanda a cewarsu yasa matsalar ke dada karuwa.

Don haka ne ma taron da aka yi a Accra na kasar Ghana kan matsalar, ya yi kira ga gwamnatocin nahiyar da su kara tashi tsaye wajen yaki da matsalar.

Bayanai sun nuna cewa a duniya akwai yara mata kimanin miliyan dari da hamsin, da kuma yara maza miliyan saba'in da uku da aka ci zarafinsu ta hanyar lalata da su, kuma mafi yawancinsu a nahiyar Afirka.

Domin tattaunawa kan batun, mun gayyato baki da suka hada da Hajiya Zainab Maina, ministar harkokin mata a Nijeriya, da Hajiya Fatima Gambo Birma, lauya ce kuma jami'a a kungiyar kare hakkin kananan yara ta Child Protection Network, CPN.

Akwai Hajiya Aisha Muhtari, wata mai kare hakkin mata da kananan yara a Ghana.

Daga Nijar kuma mun gayyaci Balkisa Diallo, shugabar kungiyar mata alkalai a Nijar, da kuma Mariama Moussa, shugabar wata kungiyar kare hakkin mata da yara kanana a Nijar. A yi sauraro lafiya: