Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Zakaran Olympics_baiwa ce ko horo?

Image caption Alamun gasar Olympics

A fagen wasanni kamar sauran fannoni na rayuwa akwai wadanda Allah(SWT) ya ba su baiwa.

Yayinda wasu gwarzayen wasan kuma sukan yi fice ne bayan samun matukar horo.

A yayinda gasar wasannin Olympics da za'ayi a birnin London ke karatowa, tambayar me mutum zai yi ya zama gwarzon wasannin Olympics ta kankane zukatan masana.

Masu ilmin sanin halayyar dan adam da masu kula da lafiya da masu horar da 'yan wasa da 'yan wasan kansu da kuma 'yan kallo na jujjuya wannan bartu a zukatansu tun shekaru aru aru.

Ga wasu, ana haihuwar shahararren dan wasa ne, saboda haduwar wasu kwayoyin halitta wadanda ke sa su, su kasance masu baiwa.

Amma ga wasu kuwa abu ne da ya shafi muhalli da abinci da kuma aiki tukuru.

Don haka ana haifuwar gwarzayen wasannin Olympics ne ko kuwa ana renonsu ne?

Shin me ke sa mutum kasancewa gwarzo?

A kan hakan ne, filin Ra'ayi Riga ya tattauna!