Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Tsarin koyar da almajirai karatun boko a Najeriya

Gwamnatin Najeriya ta bude makarantar Almajirai ta farko da za a rinka koyawa yara karatun Alkur'ani da kuma na boko a birnin Sokoto da ke Arewacin kasar.

Jami'ai sun ce wannan zai taimaka wurin rage matsalolin da Almajiran suke ciki na rashin cikakken matsuguni da kuma barace-barace.

Sai dai wasu na ganin gwamnati ta dauki matakin ne domin rage tasirin kungiyoyin addinin Musulunci a yankin.